![]() | |||||
---|---|---|---|---|---|
![]() | |||||
8 ga Yuni, 1998 - 29 Mayu 1999 ← Sani Abacha - Olusegun Obasanjo →
21 Disamba 1997 - 9 ga Yuni, 1998 | |||||
Rayuwa | |||||
Haihuwa | Minna, 13 ga Yuni, 1942 (82 shekaru) | ||||
ƙasa |
Colony and Protectorate of Nigeria (en) ![]() Taraiyar Najeriya Jamhuriyar Najeriya ta farko Jamhuriyar Najeriya ta biyu Najeriya | ||||
Harshen uwa | Gbagyi | ||||
Ƴan uwa | |||||
Abokiyar zama | Fati Lami Abubakar | ||||
Karatu | |||||
Harsuna |
Gbagyi Turanci Hausa Pidgin na Najeriya | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a | ɗan siyasa da soja | ||||
Digiri | Janar | ||||
Imani | |||||
Addini | Musulunci | ||||
Jam'iyar siyasa | no value |
Abdulsalami Abubakar, shi tsohon janar ɗin Soja ne kuma ɗan Siyasa a Najeriya da yayi mulki na ɗan lokaci sannan ya miƙawa farar hula a tsakanin shekara ta alif ɗari tara da casa'in da takwas (1998 A.c) zuwa shekarar alif ɗari tara da casa'in da tara (1999).[1] An haife shi a shekara ta alif ɗari tara da arba'in da biyu 1942 a birnin Minna, Jihar Neja dake arewacin Najeriya (a yau jihar Neja). Abdulsalami Abubakar yazama shugaban ƙasar Najeriya bayan rasuwar Janar Sani Abacha, yayi mulki daga watan Yunin shekara ta alif ɗari tara da chasa'in da takwas 1998 zuwa watan Mayun shekarar alif ɗari tara da chasa'in da tara 1999 (bayan Sani Abacha - kafin Olusegun Obasanjo).
A lokacin mulkinshi ne Najeriya ta fidda sabon kundin tsarin mulki wato 1979 constitution, wanda ta bada daman zaɓe tsakanin jam'iyyu daban daban. Abdulsalam ya miƙa madakon iko ga sabon zaɓaɓɓen shugaba Olusegun Obasanjo a ranar 29 ga watan Mayu shekara ta alif ɗari tara da chasa'in da tara 1999. Shine Chairman na yanzu na National Peace Committee.[2]