Al'adun Najeriya na gargajiya | |
---|---|
culture of an area (en) | |
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na | culture of the Earth (en) |
Facet of (en) | Najeriya |
Ƙasa | Najeriya |
Al'adar Najeriya, Ta samo asali ne daga ƙabilun Najeriya da yawa. Ƙasar tana da yaruka (harsuna) 527, bakwai daga cikinsu sun. dace. Najeriya kuma tana da yarukan da kabilu sama da guda ɗari da hamsin (1150). Manyan kabilu guda uku sune: hausawa galibinsu a arewa, yarbawa sun fi yawa a kudu maso yamma, da kuma Igbo inyamurai galibinsu a kudu maso gabas. Akwai wasu kabilun da yawa da ke da yawan mutane a fadin sassa daban-daban na kasar. Mutanen Kanuri suna yankin arewa maso gabashin Najeriya, mutanen Tiv na arewa ta tsakiya da kuma Efik - Ibibio. Mutanen Edo sun fi yawa a yankin tsakanin yankin Yarbawa da ƙasar Igbo. Yawancin Edo suna da Krista. Ana kumaaa bin wannan rukuni daga mutanen Ibibio / Annang / Efik na kudu maso kudancin Najeriya da Ijaw na Neja Delta.
Sauran kabilun Najeriya, wasu lokuta ana kiransu 'marasa rinjaye', ana samun su a duk faɗin ƙasar amma musamman a arewa ta tsakiya da kuma ɓangaren midul belt (Middle belt). A bisa ga al'ada matasa basu cika zama waje ɗaya ba (Nomadic) saboda haka Fulani za a iya samunsu a duk faɗin yammaci da tsakiyar Afirka. Fulani da Hausawa galibinsu Musulmi ne yayin da Ibo mafi yawansu kirista ne kuma haka ma mutanen Efik, Ibibio, da Annang. Yarabawa daidai suke da yuwuwar zama Krista ne ko Musulmi amma Yarbawa Musulmi sunfi kirista yawa amma ba sosai ba. Ayyukan addini na asali suna da mahimmanci ga dukkan kabilun Najeriya, kuma sau da kiristoci sunfi al'adar da ake kira (syncretism).