Anambra | |||||
---|---|---|---|---|---|
| |||||
| |||||
Suna saboda | Kogin Anambra | ||||
Wuri | |||||
| |||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | ||||
Babban birni | Awka | ||||
Yawan mutane | |||||
Faɗi | 5,527,809 (2016) | ||||
• Yawan mutane | 1,141.17 mazaunan/km² | ||||
Harshen gwamnati |
Harshen, Ibo Turanci | ||||
Labarin ƙasa | |||||
Yawan fili | 4,844 km² | ||||
Sun raba iyaka da | |||||
Bayanan tarihi | |||||
Mabiyi | Jihar Gabas ta Tsakiya | ||||
Ƙirƙira | 3 ga Faburairu, 1976 | ||||
Tsarin Siyasa | |||||
Majalisar zartarwa | Anambra State Executive Council (en) | ||||
Gangar majalisa | Majalisar dokokin Anambura | ||||
Bayanan Tuntuɓa | |||||
Lambar aika saƙo | 420001 | ||||
Kasancewa a yanki na lokaci | |||||
Tsarin lamba ta kiran tarho | +234 | ||||
Lamba ta ISO 3166-2 | NG-AN | ||||
Wasu abun | |||||
| |||||
Yanar gizo | anambrastate.gov.ng |
Jihar Anambra jiha ce dake yankin kudu maso gabashin Najeriya.[1] An kafa jihar a ranar ashirin da bakwai 27, ga watan Augustan,shekarar dubu ɗaya da ɗari tara cassa'in da ɗaya 1991.[2] Jihar Anambara ta hada iyaka da Jihar Delta daga yamma, Jihar Imo daga kudu, Jihar Enugu daga gabas, sai Jihar Kogi daga arewa.[3]
Dangane da kidayar jama'a na shekara ta dubu biyu da shida 2006, akwai mazauna garin fiye da miliyan hudu da dugo daya 4.1 a Jihar Anambra.[4] An kafa jihar ne a shekarar alif dari tara da saba'in da shida (1976) daga tsohuwar Jihar Gabas ta Tsakiya. An sanyawa jihar suna bayan rafin Kogin Anambra.[5][6] Babban birnin jihar itace Awka, birnin da ke samun yawaitar jama'a da kimanin mutum miliyan dari uku 300,000 zuwa miliyan uku 3 a tsakanin shekara ta dubu biyu da shida 2006 da shekarar dubu biyu da ashirin 2020. Birnin Onitsha, birni mai dumbin tarihi mai tashar jirgin ruwa a lokacin mulkin mallaka na turawa, wanda ya kasance har yau muhimmin cibiyar kasuwanci a jihar.[7]
Ana mata inkiya da "Fitilar Kasa" (wato "Light of the Nation"). Jihar Anambra itace jiha ta takwas a yawan jama'a a Najeriya, duk da cewa an musanta hakan sosai, bisa la'akari da cewa Birnin Onitsha ta kai kimanin miliyan 5 ta fuskar yawan a shekara ta dubu biyu da sha tara 2019.[8] Akwai tarin al'umma masu yawa a Anambra, duk da cewa itace ta biyu a karancin girma.[9][10] Yankin da aka sani a matsayin Anambra a yau ta kasance tushen cigaba na yankuna da dama tun a karni na 9 (bayan rasuwar Yesu), wanda ta hada Masarautar Nri, wacce babban birni ta itace mai dumbin tarihi na Igbo-Ukwu. Mafi akasarin mazauna Anambra Inyamurai ne.[11][12] A yau, Jihar Anambra ta kasance babban birni,[13] Kuma ta dauki matakai da dama na rage talauci.[14]