Bayelsa | |||||
---|---|---|---|---|---|
Bayelsa State (en) | |||||
| |||||
| |||||
Wuri | |||||
| |||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | ||||
Babban birni | Yenagoa | ||||
Yawan mutane | |||||
Faɗi | 2,277,961 (2016) | ||||
• Yawan mutane | 107.91 mazaunan/km² | ||||
Harshen gwamnati | Turanci | ||||
Labarin ƙasa | |||||
Yawan fili | 21,110 km² | ||||
Sun raba iyaka da | |||||
Bayanan tarihi | |||||
Mabiyi | Jihar rivers | ||||
Ƙirƙira | 1 Oktoba 1996 | ||||
Tsarin Siyasa | |||||
Majalisar zartarwa | Executive Council of Bayelsa State (en) | ||||
Gangar majalisa | Bayelsa State House of Assembly (en) | ||||
Bayanan Tuntuɓa | |||||
Kasancewa a yanki na lokaci | |||||
Lamba ta ISO 3166-2 | NG-BY | ||||
Wasu abun | |||||
| |||||
Yanar gizo | bayelsastate.gov.ng |
Jihar Bayelsa jiha ce dake kudu maso kudancin Najeriya, tana nan a tsakiyar yankin Niger Delta.[1][2] An kirkiri Jihar Bayelsa[3] ne a shekarar alif dubu daya dari Tara da casa'in da shida (1996), kuma an cire ta ne daga Jihar Rivers.[4] Hakan yasa ta zamo daya daga cikin sabbin jihohin kasar. Ta hada iyaka da Jihar Rivers[5] daga gabas, da kuma Jihar Delta daga yamma, inda Tekun Atalanta[6] ta mamaye yankin kudancin jihar.[2]
Jihar Bayelsa nada fadin fili na kimanin kilomita 10,773kmaq, wanda yasa ta zamo jiha mafi karancin fili a Najeriya.[7] Kuma tana da yawan jama’a kimanin mutum 2,394,725, (kiyasin shekara ta 2016), wanda ya sanya ta jiha mai mafi karancin mutane. Babban birnin jihar, itace Yenagoa. Douye Diri ne gwamnan jihar a shekara ta 2022, mataimakin shi kuma shine Lawrence Ewhrudjakpo.[8] Dattijan jihar sun hada da: Goodluck Jonathan, David Clark, Ben Murray Bruce, Emmanuel Paulker Izibefien da Evan Foster Ogola. A sanadiyyar kasancewarta a yankin Niger Delta, Jihar Bayelsa mamaye take da kogi da koramu, kuma kusan duka garin cikin ruwa yake, hakan ya jawo rashin cigabanta ta hanyar gina hanyoyi.[9]
Ana amfani da harshen Ijaw a ko ina a jihar, tare da sauran harsuna kamar Isoko da Urhobo a tsaffin kyaukan jihar.
Tana da kanan hukumomi 8: Ekeremor, Kolokuma/Opokuma, Yenagoa, Nembe, Ogbia, Sagbama, hi Brass da kuma Ijaw kudu. Bayelsa ta kasance gida ga Mutanen Urhobo a karamar hukumar Sagbama.[10]
A dalilin kasancewarta a yanki mai arzikin man-fetur wato Niger Delta, tattalin arzikin Jihar Bayelsa sun ta'allaka ne akan haka man-fetur da ma'aikatun tace su. Yankin Oloibiri Oilfield inda aka fara hako man fetur a Najeriya.[11] Sannan zuwa shekara ta 2015, an kiyasta cewa tana samar da kusan kashi 30-40% na man fetur din Najeriya.[12] Ana yiwa jihar lakabi da “Glory of all Lands” sannan ita ke da tafkin gas mafi girma a Najeriya (18 trillion cubic feet).[13] Duk da cewa jihar ta mallaki manyan rijiyoyin mai kuma tana taka muhimmiyar rawa wajen cigaban tattalin arzikin kasa, talauci yayi wa jihar katutu, hadi da gurbacewar muhalli[14] daga fesowar man fetur.[15][16]