Bola Tinubu | |||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|
29 Mayu 2023 - ← Muhammadu Buhari
29 Mayu 1999 - 29 Mayu 2007 ← Mohammed Buba Marwa - Babatunde Fashola →
| |||||||
Rayuwa | |||||||
Cikakken suna | Bola Ahmed Tinubu | ||||||
Haihuwa | Lagos,, 29 ga Maris, 1952 (72 shekaru) | ||||||
ƙasa | Najeriya | ||||||
Ƙabila | Yaren Yarbawa | ||||||
Harshen uwa | Yarbanci | ||||||
Ƴan uwa | |||||||
Mahaifiya | Abibatu Mogaji | ||||||
Abokiyar zama | Oluremi Tinubu | ||||||
Karatu | |||||||
Makaranta | Chicago State University (en) | ||||||
Harsuna |
Turanci Yarbanci | ||||||
Sana'a | |||||||
Sana'a | accountant (en) , ɗan siyasa da shugabani ƙasar Najeriya | ||||||
Employers |
Arthur Andersen (en) GTE (en) Deloitte (en) Mobil Producing Nigeria (en) | ||||||
Imani | |||||||
Addini | Musulunci | ||||||
Jam'iyar siyasa |
Alliance for Democracy (en) Action Congress of Nigeria All Progressives Congress |
Bola Ahmed Adekunle Tinubu an haife shi a ranar 29 ga watan Maris a shekara ta alif dubu ɗaya da Ɗari Tara da hamsin da biyu (1952) Miladiyya. Bola Ahmed Adekunle Tinubu ya kasance kwararren ɗan siyasar Najeriya, kuma shugaban ƙasar Najeriya tun daga ranar 29 ga watan mayun shekara ta 2023.[1] Ya yi aiki a matsayin Gwamnan jihar Legas daga shekarata alif dubu ɗaya da Ɗari Tara da casa'in da Tara (1999) zuwa shekarata dubu biyu da bakwai (2007), haka yayi Sanata mai wakiltar Legas ta yamma na wani gajeren lokaci a jamhuriya ta uku (Third republic).[2]
Bola Ahmed Tinubu shahararran ɗan siyasa ne a Najeriya wanda ke da sarautar Asiwaju a kasar Yarabawa, kuma Jagaban a Borgu ta Jihar Neja, ya shahara a fagen siyasa da mulki a Najeriya baki daya.
Ana kallon Asiwaju a matsayin wanda ya dade yana jan zarensa tun daga dawowar Najeriya kan mulkin demokaradiyya ta alif dubu daya da dari Tara da casa'in da Tara (1999), Tinubu ya kasance a matsayin uba a fagen siyasa sakamakon karfin fada a ji da yake da shi a siyasar kasar ta Yarbawa da ma Najeriya baki daya.
Haka kuma ya kafa mutane da dama a Najeriya inda ya yi musu hanya suka samu mukamai a tarayya da jihohi. Ihayatu ( talk) 21:37, a ranar 30 ga watan Mayu shekarata 2023 (UTC)) [3][4][5]