CNN,(Cable News Network) tasharwatsalabarai ce ta ƙasa da ƙasa mai hedikwata a Atlanta, Jojiya, Amurka.[1][2][3] An kafa ta a cikin shekarata 1980 ta hannun mai mallakar kafofin watsa labarai na Amurka Ted Turner da Reese Schonfeld a matsayin tashar watsa labarai na tsawon sa'o'i 24 a kullum, kuma a halin yanzu mallakar kamfanin na watsa labarai na hannun Manhattan, Warner Bros. Discovery.[4] CNN ita ce tashar talabijin ta farko da ta fara watsa labarai tsawon sa'o'i 24. Kuma tashar talabijin ta farko- da ta fara watsa labarai a Amurka.[5][6][7][8][9]
Tun daga watan Satumba na shekarar 2018, CNN tana da masu mu'amala (subscribers) da tashar mutane miliyan 90.1 a matsayin masu biyan kuɗi (subscriptions), kuma (kashi 97.7% cikin 100 na masu mu'amala da tashar, na da tashar acikin akwatunan telebijin nasu a gidajen su).[10] MSNBC, matsakaicin masu kallo 580,000 a ko'ina cikin yini, ya ragu da kashi 49% daga shekarar da ta gabata, a cikin raguwar masu kallo a duka hanyoyin sadarwar tashar (channels).[11] Yayin da CNN ke a matsayi na 14 a cikin jerin tashoshin watsa labarai a shekara ta 2019,[12][13] gidan telebijin ɗin yayi kukan kura inda ya zabura izuwa mataki na 7th daga mataki na 14 da yake abaya. Acikin manyan hanyoyin sadarwa da sukayi fice akwai; (Fox News a mataki na 5, da MSNBC a mataki na 6, a wannan shekarar),[14] ta koma mataki na 11 a shekarar 2021.[15]
A duk duniya, shirye-shiryen CNN ana watsawa ta hanyar CNN International, waɗanda masu kallo ke gani a cikin ƙasashe da yankuna sama da 212;[16] tun daga watan Mayu 2019. Gidan talabijin ɗin mallakar Amurka, ana takaita sunan da CNN (US), Bugu da ƙari tana watsa shirye-shiryen ta a Kanada, wasu tsibiran Caribbean da kuma a Japan, inda aka fara watsa shirye-shirye a kafar yaɗa labarai ta CNNj a shekara ta 2003, tare da fassarar lokaci guda cikin harshen Jafananci.[17]