Daular Usmaniyya (Larabci دولت عليه عثمانیه), (Turanci Devlet-i ʿAlīye-i ʿOsmānīye), (TuranciExalted Ottoman State), (Turanci na wannan zamani; Osmanlı İmparatorluğu, ko Osmanlı Devleti), (Faransanci Empire ottoman),[1][1][2] daula ce da akayi ta a ƙasar mai mazauni a ƙasar Turkiyya a yanzu wadda taɗau tsakanin lokacin 1299 zuwa 1923. Daular na zaune a Turkiyya kuma tana da iko da gabashi da kudancin ƙasashen dake a gefen kogin Meditereniya.
Tsakanin shekara ta 1299 Osman I ya kafa daular, kuma tayi ƙarfi sosai tsakanin shekara ta 1400 zuwa shekarar 1600, lokacin ƙarfin ikon ta ya mamaye yankunan kudu maso gabashin Turai da kudu maso Yammacin Asiya da kuma arewacin Afrika.
Daular ta samu ne sakamakon cinye kasashe da yaki. Sarki ne ke aikawa da Gwamna zuwa dukkan kasar da daular ta kama domin yayi shugabanci, ana kiran wadannan gwamnonin da Pasha ko Bey. Mafi shahara daga cikin su a ƙarni na 19 shine Muhammad Ali Pasha.
Daular Usmaniyya ta karye ne a lokacin Yaƙin Duniya na I wanda yayi sanadin dukkan ƙasashen kowacce ta rabu da juna.