Edo | |||||
---|---|---|---|---|---|
| |||||
| |||||
Wuri | |||||
| |||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | ||||
Babban birni | Birnin Kazaure | ||||
Yawan mutane | |||||
Faɗi | 4,235,595 (2016) | ||||
• Yawan mutane | 237.93 mazaunan/km² | ||||
Harshen gwamnati | Turanci | ||||
Labarin ƙasa | |||||
Yawan fili | 17,802 km² | ||||
Sun raba iyaka da | |||||
Bayanan tarihi | |||||
Mabiyi | Bendel State (en) | ||||
Ƙirƙira | 27 ga Augusta, 1991 | ||||
Tsarin Siyasa | |||||
Majalisar zartarwa | Executive council of Edo State (en) | ||||
Gangar majalisa | Edo State House of Assembly (en) | ||||
Bayanan Tuntuɓa | |||||
Lambar aika saƙo | 300001 | ||||
Kasancewa a yanki na lokaci | |||||
Tsarin lamba ta kiran tarho | +234 | ||||
Lamba ta ISO 3166-2 | NG-ED | ||||
Wasu abun | |||||
| |||||
Yanar gizo | edostate.gov.ng |
Jihar Edo Jiha ce dake kudu maso kudancin Najeriya.[1] Babban birnin jihar shi ne Benin. Dangane da ƙidayar shekara ta 2006, Jihar ita ce ta shida a yawan jama'a da adadin mutane kimanin 3,233,366.[2] Edo ita ce ta 22 a faɗin ƙasa a Najeriya.[3] Babban birnin jihar shi ne Benin City, ita ce birni ta hudu a girma a Najeriya, kuma ta ƙunshi cibiyar masana'antun roba a Najeriya.[4][5] An ƙirƙire ta a shekarar 1991, daga tsohuwar Jihar Bendel, kuma ana kiranta da kuma suna "Heart beat of the Nation" (bugun zuciyan ƙasa).[6]
Jihar Edo tana da iyaka da Jihar Kogi daga arewa maso gabas, Jihar Anambra da ga gabas, Jihar Delta daga kudu maso gabas da kudu maso kudancin jihar, Jihar Ondo kuma daga yamma.[7]
Yankunan Jihar Edo a yau sun haɗa iyaka da masarautun da dauloli da aka kafa tun a ƙarni na 11 miladiyya, harda Masarautar Benin.[8] A shekarar alif 1897, Daular Burtaniya ta ƙaddamar da wata azzalimar ziyara ga yankin Benin, inda suka tarwatsa tsaffin biranen Edo, inda suka haɗe su a cikin yankin da ta zamo Yankin mulkin mallaka na Kudancin Najeriya.[9][10]
Edo jiha ce dake ɗauke da mutane iri-iri musamman Harsunan Edoid da kuma Mutanen Edo ko Bini,[11] Esan, Kabilar Owan, Afemai.[12] Harshen da yafi fice daga cikin yarukan Edo shine Yaren Edo wanda akae yawan amfani dashi a Birnin Benin.[13] Mafi yawa mutanen Jihar mabiya addinin Kiristanci ne. Turawan mishanari na Portugal suka kawo addinin a yankin a ƙarni na 15. Akwai 'yan tsirarun mabiya addinin Musulunci da addinan gargajiya.[14]