Farooq Kperogi | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Baruten, 30 ga Maris, 1973 (51 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Karatu | |
Makaranta |
Georgia State University (en) University of Louisiana at Lafayette (en) Jami'ar Bayero |
Harsuna | Turanci |
Sana'a | |
Sana'a | linguist (en) , Malami da ɗan jarida |
farooqkperogi.com |
Farooq Adamu Kperogi (An haifeshi ranar 30 ga watan Maris din Shekarar 1973) tshohon ɗan jarida ne kuma malamin ilimin hanyoyin sadarwa na zamani a kasar Amurka. Farooq yayi aikin jarida a gidaje jaridun Najeriya kamar Daily Trust da kuma tsohuwar jaridar New Nigerian ta gwamnatin tarayya da kuma Daily Triumph.[1]
Kperogi yana cikin masu rubuta jawabin shugaban kasa a zamanin mulkin Obasanjo, kuma ya koyar da aikin jarida a Jami'ar Ahmadu Bello da Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kaduna. Yana koyar da aikin jarida a Jami'ar Jihar Kennesaw da ke Jojiya, Amurka.[2][3][4] Shi ne kuma marubucin (Glocal English: The Changing Face and Forms of Nigerian English), wanda aka buga a cikin shekara ta 2015, a matsayin juzu'i na 96 a cikin jerin Insights na Berkeley a cikin Linguistics da Semiotic.[5][6]