![]() | |
---|---|
public office (en) ![]() ![]() | |
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na |
governor of a Nigerian state (en) ![]() |
Bangare na | Majalisar zartaswa ta jihar Kaduna |
Farawa | 27 Mayu 1967 |
Ƙasa | Najeriya |
Applies to jurisdiction (en) ![]() | Jihar Kaduna |
Substitute/deputy/replacement of office/officeholder (en) ![]() |
Deputy Governor of Kaduna State (en) ![]() |
Gwamnan jihar Kaduna shine shugaban gwamnatin kaduna. Gwamna shine ke jagorantar bangaren zartarwa na Gwamnati. Wannan matsayi ya sanya mai riƙe shi a jagorancin jihar tare da ikon sarrafawa akan al'amuran jihar. Ana yawan bayyana Gwamna a matsayin ɗan ƙasa mai lamba ta ɗaya na jihar. Mataki na biyu na Kundin Tsarin Mulki na Najeriya ya bada ikon zartarwa na jihar a cikin gwamna kuma ya umurce shi da aiwatar da dokar jihar, tare da alhakin nada shugabannin zartarwa, na diflomasiyya, na doka, da na jami'an shari'a bisa amincewar mambobin Majalisar. Ana zaban gwamnan jihar zuwa ofishi a yayin gudanar da zaben kasa ta hanyar dimokiradiyya, Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ce ke shirya zaben, kuma ana gudanar da shi bayan duk bayan shekaru hudu na wani wa’adi. Gwamna zai iya takarar ofis sau biyu ne kawai idan ya ci nasara, a wata ma'anar, zai share tsawon shekaru takwas a kan mulki (zango biyu).