Jahar Taraba | |||||
---|---|---|---|---|---|
| |||||
| |||||
Wuri | |||||
| |||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | ||||
Babban birni | Jalingo | ||||
Yawan mutane | |||||
Faɗi | 3,066,834 (2016) | ||||
• Yawan mutane | 56.3 mazaunan/km² | ||||
Harshen gwamnati | Turanci | ||||
Labarin ƙasa | |||||
Yawan fili | 54,473 km² | ||||
Sun raba iyaka da | |||||
Bayanan tarihi | |||||
Mabiyi | Jihar Gongola | ||||
Ƙirƙira | 27 ga Augusta, 1991 | ||||
Tsarin Siyasa | |||||
Majalisar zartarwa | Majalisar Zartarwa ta Jihar Taraba | ||||
Gangar majalisa | Taraba State House of Assembly (en) | ||||
Bayanan Tuntuɓa | |||||
Lambar aika saƙo | 660001 | ||||
Kasancewa a yanki na lokaci | |||||
Tsarin lamba ta kiran tarho | +234 | ||||
Lamba ta ISO 3166-2 | NG-TA | ||||
Wasu abun | |||||
| |||||
Yanar gizo | tarabastate.gov.ng |
Taraba (Fula: Leydi Taraba) jiha[1] ce a Arewa maso Gabashin Najeriya[2], sunanta daga sunan Kogin Taraba, ta ratsa kudancin Jihar. Babban birnin Jihar shi ne Jalingo[3]. Mazauna a jihar galibinsu ƙabilun Mumuye da Fulani[4] da Jukunawa da Marghi da Jenjo da Wurkum da kuma wasu ƙabilu dake a yankin Arewacin Jihar. Yayin da Jukun, Chamba, Tiv, Kuteb da Ichen waɗanda aka fi samun su a yankin kudancin jihar. Yankin tsakiyar ya fi mamaye mutanen Mambila, Chamba, Fulani da Jibawa. Akwai sama da ƙabilu saba'in da bakwai (77) masu mabanbantan harsuna a jihar Taraba da addinai kamar Christian da Musulmi.