Jemage | |
---|---|
Scientific classification | |
Subkingdom | Bilateria (mul) ![]() |
Phylum | Chordata |
Class | Mammalia (mul) ![]() |
Superorder | Laurasiatheria (mul) ![]() |
order (en) ![]() | Chiroptera Blumenbach, 1779
|
Geographic distribution | |
![]() | |
General information | |
Tsatso |
bat meat (en) ![]() |
Tsawo | 6 ft da 1 in |
Audible frequency range |
2,000 hertz (en) ![]() ![]() |
Jemage halitta ce dake a cikin nau'ukan halitta na mammals, wasu na zacin jemage amatsayin tsuntsu, amma ba'a dangin tsuntsaye yake ba. Jemage na daya daga cikin dabbobi masu shayarwa na tsarin Chiroptera (/kaɪˈrɒptərə/).[1] suna amfani da ƙwaƙƙwaran gabansu, wato gabobin su na farko a matsayin fuka-fuki, su ne kawai dabbobi masu shayarwa waɗanda ke shawagi mai dorewa. Jemage sun fi saurin tashi sama fiye da yawancin tsuntsaye, suna tashi da yatsun su masu tsayi da yalwa wanda suke lulluɓe da siraran nama.
Jemagu sun kasance a tsari na biyu mafi girma na dabbobi masu shayarwa bayan Beraye, sun kuma ƙunshi kusan kashi 20% na dukkan nau'ikan dabbobi masu shayarwa a duniya, fiye da nau'ikan 1,400. An raba waɗannan a gargajiyance zuwa gida biyu: Manyan-jemage (megabats) masu cin 'ya'yan itace da masu amfani da amsawar sauti domin gane inda abu yake wato Kananun-jemage (Microbats). Yawancin jemagu suna cin kwari ne, wasu kuma suna cin 'ya'yan itace ko furanni. kadan daga ciki ne suke cin wani abu daga dabbobi banda kwari; misali, jemage mai shan jini, wanda ya kasance yana tsutsar jini daga jikin dabbobi. Yawancin jemagu 'Yan-dare ne, kuma da yawa suna zama a cikin kogo ko wasu mafaka; Babu tabbas ko jemagu suna da waɗannan halayen domin tsira daga mafarauta. Jemage suna nan a duk faɗin duniya, ban da yankuna masu tsananin sanyi.