Our website is made possible by displaying online advertisements to our visitors.
Please consider supporting us by disabling your ad blocker.

Responsive image


Jukunawa

Jukunawa

Yankuna masu yawan jama'a
Najeriya

Jukunawa ( Njikum ) ƙungiya jam'a ce ta yare ko harsuna a Afirka ta Yamma. 'Yan kabilar Jukun suna zaune a al'adance a jahohin Taraba, Benue, Nasarawa, Filato, Adamawa, da Gombe a Najeriya da wasu sassan arewa maso yammacin Kamaru. Sun fito ne daga tsatson mutanen Kwararafa. Yawancin ƙabilun da ke arewacin tsakiyar Najeriya sun samo asalinsu ne daga ƙabilar Jukun kuma suna da alaƙa ta wata hanyar da harshen Jukun. Har zuwa zuwan Kiristanci da Musulunci, mutanen Jukun mabiya Addinin Gargajiya ne, Mafi yawan kabilun, Alago, Agatu, Rendere, Goemai a Shendam, da sauransu sun bar Kwararafa lokacin da ta wargaje sakamakon wani rikici da ya ɓarke. Mutanen Jukun sun kasu kashi biyu manyan rukuni; da Jukun Wanu da Jukun Wapa. Jukun Wanu masunta ne da ke zaune a gabar kogin Benuwai da Neja inda suke ratsawa ta jihar Taraba, da jihar Benuwai da kuma jihar Nasarawa .[ana buƙatar hujja] Ƙungiyar Wukari, ƙarƙashin jagorancin Aku Uka na Wukari, yanzu ita ce babbar cibiyar jama'ar Jukun.


Previous Page Next Page






شعب جوكون ARZ Jukuns Catalan Jukun people (West Africa) English Jukun Spanish Jukun (peuple) French Ndị obodo jukun (West Africa) IG Jukun Italian Джукун KK Джукун (эл) KY Dżukunowie Polish

Responsive image

Responsive image