Our website is made possible by displaying online advertisements to our visitors.
Please consider supporting us by disabling your ad blocker.

Responsive image


Katsina (jiha)

Katsina
Katsina State (en)
Jihar Katsina (ha)


Wuri
Map
 12°15′N 7°30′E / 12.25°N 7.5°E / 12.25; 7.5
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya

Babban birni Jahar Katsina
Yawan mutane
Faɗi 7,831,319 (2016)
• Yawan mutane 323.72 mazaunan/km²
Harshen gwamnati Turanci
Labarin ƙasa
Yawan fili 24,192 km²
Sun raba iyaka da
Bayanan tarihi
Mabiyi Jihar Kaduna
Ƙirƙira 23 Satumba 1987
Tsarin Siyasa
Majalisar zartarwa Majalisar Zartarwa ta Jihar Katsina
Gangar majalisa Katsina State House of Assembly (en) Fassara
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci
Lamba ta ISO 3166-2 NG-KT
Wasu abun

Yanar gizo katsinastate.gov.ng
Katsina State Inland Revenue Office, Katsina City
Fadar sarkin katsina
Gobarau minaret katsina

Katsina jiha ce a shiyyar Arewa Maso Yammacin Najeriya.[1] An kuma ƙirkiri jihar Katsina ne a shekarar 1987, lokacin da aka samar da ita daga jihar Kaduna. A yau, Jihar Katsina ta yi iyaka da Jihohin Zamfara da Kaduna da Kano da Jigawa, har ila yau Kuma Katsina tanada iyaka da Jamhuriyar Nijar. Ana yi mata laƙabi da "Ta Dikko Ɗakin Kara", kuma ana yi wa Katsinawa kirarin "Kunya gareku ba dai tsoro ba".Babban birnin jihar da garin Daura, an bayyana su daga cikin "tsofaffin mazaunun al'adu da Musulunci da kuma ilmantarwa" a Najeriya.

Jihar Katsina, tana da mazauna har sama da 5,800,000 a ƙidayar shekarar 2006, Jihar Katsina ce ta biyar (5) mafi girma acikin Jerin yawan haɓakar jama'a a jihohi biyar mafi girma a cikin ƙasar ta Nijeriya, cikin yawan jama'a, duk da kasancewarta ta bakwai daga cikin Jihohi 17 mafi faɗin ƙasa daga cikin jihohi 36 na tarayyar Nijeriya. Ta fuskar adadin ƙabilu kuwa, jama'a, Fulani sun fi kowace ƙabila yawa a jihar, kuma mafi yawancin mutanen Jihar Katsina suna bin koyarwar addinin Musulunci. A shekarar 2005, [2] A shekarar 2005,[3][4]Katsina ta zama jiha ta biyar a Najeriya da ta yi amfani da tsarin Shari'ar Musulunci.

Gwamnan jihar Katsina na yanzu shi ne Dr.Dikko umar radda, dan jam’iyyar "All Progressives Congress"Ana ɗaukar Jihar a matsayin babbar cibiyar siyasar Muhammadu Buhari, ɗan asalin garin Daura, wanda ya lashe a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2019 da kusan kashi 80% na ƙuri’un mutanen jihar. [5]

Jihar Katsina na ɗaya daga cikin Jihohin Najeriya da ke fama da matsalar ta'addanci. Wacce ta fara a shekarar 2020. Kungiyar yan ta'adda da yan fashi da garkuwa da mutane sun yi garkuwa da yara sama da 300 a ƙaramar hukumar kankara.[6][7]

  1. "Home | Institute of International Studies". iis.berkeley.edu. Retrieved 2021-03-07.
  2. Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named ahram
  3. "CNN.com - Woman sentenced to stoning freed - Feb. 23, 2004". edition.cnn.com. Retrieved 2021-03-07.
  4. "Katsina adopts Sharia". The New Humanitarian (in Turanci). 2000-08-01. Retrieved 2021-03-07.
  5. "Buhari Wins Katsina with 1.2m Votes". THISDAYLIVE (in Turanci). 2019-02-25. Retrieved 2021-03-07.
  6. "More than 300 schoolchildren are abducted in Nigeria". The Economist. 2020-12-19. ISSN 0013-0613. Retrieved 2021-03-07.
  7. "Gunmen kidnap 'hundreds' of schoolboys in central Nigeria". France 24 (in Turanci). 2021-02-17. Retrieved 2021-03-07.

Previous Page Next Page