![]() | |||||
---|---|---|---|---|---|
الخلافة الراشدة (ar) | |||||
|
|||||
| |||||
Wuri | |||||
| |||||
Babban birni | Madinah da Kufa | ||||
Yawan mutane | |||||
Harshen gwamnati | Larabci | ||||
Addini | Musulunci | ||||
Labarin ƙasa | |||||
Bangare na | Khalifofi | ||||
Bayanan tarihi | |||||
Mabiyi |
Medina community (en) ![]() | ||||
Wanda ya samar | Sayyadina Abubakar | ||||
Ƙirƙira | ga Yuni, 632 | ||||
Rushewa | 28 ga Yuli, 661 | ||||
Ta biyo baya | Khalifancin Umayyawa | ||||
Tsarin Siyasa | |||||
Tsarin gwamnati |
elective monarchy (en) ![]() | ||||
• Khalifofi shiryayyu | Sayyadina Abubakar (6 ga Yuni, 632) | ||||
Ikonomi | |||||
Kuɗi |
dinar (en) ![]() |
Khula'hur-Rashidun (a Larabci, Khilafa-al-Raahidah آلخلافة ألراشدة) Sune Kalifofin farko guda hudu ko kuma magada na jagorancin Daular Musulunci tun bayan Wafatin fiyayye halitta Annabi Muhammad (s.a.w) a shekara ta 632M wato 11H. Khulafa'ar-Raahidun sune sukayi shugabancin Daular Musulunci daga 632-661M. Musulmai mabiya Sunnah wato Sunni Islam ne ke kiran su da sunan Khulafa'hur-Rashidun, amma a bangaren mabiya Shi'a wannan kalmar bata amfani domin kuwa sun hakikance da Kalifofin ukun farko kafin Sayyadina Ali sunyi kwace ne, kuma basa ganin su da girmamawa.
Khulafa'hur-Rashidun sunyi kalifanci ne na shekara 25
Bayan Wafati Annbi (s.a.w) ne sahabban sa suka fara tattaunawa game da ko wanene zai gaje shi wajen jagorancin musulmai a yayinda sukuma iyalan gidansa suna can suna shirya Janazar sa. Sayyadina Umar da Abu Ubaidullah ibn al-jarrah suka nuna mubaya'ar su ga Sayyadina Abubakar.