Konfushiyanci | |
---|---|
Mai kafa gindi | Confucius |
Classification |
|
Practiced by | Confucian scholar (en) |
Branches |
Confucianism in Japan (en) Confucianism in Indonesia (en) Neo-Confucianism (en) Korean Confucianism (en) Three virtues of Confucianism (en) Three Essentials and Five Virtues (en) |
Konfushiyanci shine falsafar da ke kan koyarwar Konfushiya (551 BC - 479 BC), wanda ya kasance babban masanin falsafar kasar Sin . Konfushiyanci yanada cikakken tsarin tunanin ɗabi'a, zamantakewa, siyasa, da tunani na addini, kuma yana da babban tasiri a tarihin wayewar ƙasar Sin . Wasu mutane suna ganin yakamata a kira addini na Konfushiyanci amma wasu basu yarda ba.
An yi Konfushiyanci don dakatar da faɗuwar al'ummar Sin. Bayan daular Zhou ta faɗi, mutane sun damu da kansu kawai kuma ba sa girmama wasu. Konfushiyanci ya zama tsarin zamantakewa ga kasar Sin, yana koyar da cewa alakar zamantakewa ita ce mafi mahimmanci. Mutane sannu a hankali sun fara yin imani da shi, saboda suna son samun zaman lafiya, amma su ma sun kula da kansu. A sakamakon haka, Konfushiyanci ya kawo wa mutane ƙauna, jituwa, da girmama juna.
An fara koyar da Konfushiyanci a Ch'u-fu, mahaifar Konfushiya. A yau, Konfushiyanci ya bazu ko'ina cikin duniya, amma har yanzu yana da mahimmanci a China.
Koyaswar Konfushiya ta fi mayar da hankali kan girmama iyayen mutum, dattawa, da kakanni. Ya kuma koyar da cewa mutane 'ba za su taɓa daina koyo ba'; ma'ana ilimi ba shi da iyaka, saboda haka koyaushe za mu koya, ba za mu daina ba. Misali, ya taba tambayar yaro dan shekara bakwai ya zama malaminsa, saboda yaron ya san wani abu da bai sani ba.