Kuka | |
---|---|
Scientific classification | |
Kingdom | Plantae |
Order | Malvales (en) |
Dangi | Malvaceae (en) |
Genus | Adansonia |
jinsi | Adansonia digitata Linnaeus, 1759
|
General information | |
Tsatso | bouye (en) , baobab seed oil (en) da baobab leaf (en) |
Kuka (kúúkà) (Adansonia digitata) bishiya ce.[1] Kuka bishiya ce mai tsayi da take da ganye launin kore tana girma a ƙasashe da dama a nahiyar Afrika inda ƙasar Senegal ta kasance gaba a cikin sahun jerin ƙasashen dake noma ta inda har fitar da ita suke yi domin su sayar ga wasu ƙasashe. A jihohin Arewacin Najeriya, yankin Zuru dake a jihar Kebbi na daga cikin manyan wuraren dake noman kuka inda ko bayan amfanin da suke yi da ita har fitar da ita suke yi suna sayarwa.