![]() | |
---|---|
sana'a | |
![]() | |
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na |
humanities scholar (en) ![]() |
Field of this occupation (en) ![]() | falsafa |
Yana haddasa | tarihin falsafa |
Patron saint (en) ![]() |
Catherine of Alexandria (en) ![]() ![]() ![]() |
Nada jerin |
list of philosophers (en) ![]() |
Mafalsafi ko mai falsafa shine masanin falsafa wanda kuma yake aiki da falsafar . Kalmar Falsafa ta fito ne daga daɗaɗɗar Girka: Philosophos, ma'ana 'masoyin hikima'. Ƙirƙirar kalmar an danganta ta ga manazarcin Girka mai suna Pythagoras (a ciken ƙarni na 6 KZ).
A kilasikiyance, mafalsafi shi ne wanda ya rayu bisa ga wata hanya ta rayuwa, yana mai da hankali kan warware tambayoyi na wanzuwa game da yanayin ɗan adam ; ba lallai ba ne su yi magana a kan ra'ayoyin ko yin sharhi kan marubuta. [1] Waɗanda suka sadaukar da kansu ga wannan salon rayuwa da an ɗauke su a matsayin mafalsafa, kuma yawanci sun bi falsafar Hellenanci .
A ma'anar zamani, mafalsafi intelekcuwal ne wanda ke ba da gudummawa ga ɗaya ko fiye da ɗaya na rassan falsafa, kamar su aesthetics, ɗa'a, efistomalojiya, falsafar kimiyya, lojik, fiziyarmeta, Nazariyar zamantakewa, falsafar addini, falsafar siyasa . Masanin falsafa kuma yana iya zama wanda ya yi aiki a cikin ilimin ɗan adam ko wasu ilimomin kimiya waɗanda a cikin ƙarnukan da suka wuce suka rabu da falsafar, kamar fasaha, tarihi, tattalin arziki, ilimin zamantakewa, soshiyolojiya, ilimin harshe, anturofolojiya, tiyoloji, da siyasa .