nahiya | |
---|---|
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na | landmass (en) da natural geographic object (en) |
Bangare na | Earth's crust (en) da Duniya |
Ƙasantuwa a yanayin ƙasa | continental crust (en) |
Described at URL (en) | whosonfirst.org… |
Hannun riga da | ocean (en) |
Nahiya na nufin manya-manyan da'irar shimfiɗaɗɗun ƙasashe da ake da su a duniya. Akan ƙididdige su ne dangane da yarjejeniya ba wai don wasu ƙa'idoji na musamman ba, akwai yankuna na ƙasa guda bakwai wanda ake ɗauka a matsayin nahiyoyin duniya. Wanda aka jera su daga mafi girmansu zuwa mafi ƙanƙantansu, waɗannan nahiyoyi bakwai sune: Asiya, Afirka, Amurka ta Arewa, Amurka ta Kudu, Antatika, Turai, Ostiraliya.[1] Wasu 'yan bambance-bambance na iya haɗe wadannan nahiyoyi misali, Amurka, Eurasia, ko kuma Afro-Eurasia akan dauke su a wasu lokutan a matsayin nahiya ɗaya wadanda ka iya rage yawan nahiyoyin zuwa guda huɗu.
Amma abin da aka fi haƙƙaƙewa akai shi ne, waɗannan nahiyoyi guda Bakwai ne. Kuma sun haɗar da Afirka da Antatika da Asiya da Ostraliya da Turai da kudancin Amirka da kuma Arewacin Amirka. Wannan a yadda aka karantar da ɗalibai kenan a yankin nahiyar Amirka baki ɗaya. Ana daukan Zealandia, wani katafaren yanki na duniya a matsayin nahiya mai zaman kanta.
Amma kuma a yankin nahiyar Turai da kuma sauran sassan duniya, mafi yawan ɗaliban yankunan ana karantar da su cewar, nahiyoyi Shida rak ake da su a duniyar nan. Ma'ana a waɗannan yankuna ana duban Kudancin Amirka da kuma Arewacin Amirka a matsayin nahiya guda ɗaya ta Amirka. Anan lissafin nahiyoyi shidan kenan ya haɗar da Afirka da Amirka da Antarctica da Asiya da Australiya da kuma Turai.
To sai dai a halin da ake ciki kuma, mafiya yawan masana ta fuskar kimiyya na duban waɗannan nahiyoyi Shida da cewar nahiyar Turai da ta Asiya a dunƙule suke wuri ɗaya a matsayin nahiya guda, don haka ne ma suke kiran nahiyar da suna Eurasiya, sai kuma Afirka da Antarctica da Austaraliya da Kudancin Amirka da kuma Arewacin Amirka.
Masana ilimin taswirar duniya, su kuma a halin yanzu sun kasafta duniyar nan zuwa yankuna takwas domin samun sauƙin fahimta. Yanki na farko dai shi ne na Asiya, wanda ya ƙunshi Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afirka. Sai kuma Turai da Arewacin Amirka. Akwai kuma Tsakiyar Amirka da yankin Carribbean, kana kuma Kudancin Amirka da Afirka da Austaraliya da kuma Yankin Teku, wato Oceania kenan.