Port Harcourt | |||||
---|---|---|---|---|---|
| |||||
| |||||
Suna saboda | Lewis Harcourt, 1st Viscount Harcourt (en) | ||||
Wuri | |||||
| |||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | ||||
Jihohin Najeriya | Jihar rivers | ||||
Ƙananan hukumumin a Nijeriya | Port Harcourt (karamar hukuma) | ||||
Babban birnin | |||||
Yawan mutane | |||||
Faɗi | 3,325,000 (2022) | ||||
• Yawan mutane | 9,236.11 mazaunan/km² | ||||
Labarin ƙasa | |||||
Bangare na | South South (en) | ||||
Yawan fili | 360 km² | ||||
Wuri a ina ko kusa da wace teku | Tekun Guinea | ||||
Altitude (en) | 18 m-18 | ||||
Sun raba iyaka da | |||||
Bayanan tarihi | |||||
Ƙirƙira | 1912 | ||||
Bayanan Tuntuɓa | |||||
Lambar aika saƙo | 500101 to 500272 | ||||
Kasancewa a yanki na lokaci | |||||
Tsarin lamba ta kiran tarho | +234 |
Port Harcourt Birni ne, da ke a jihar Rivers, a kasar Najeriya. Shi ne babban birnin jihar Rivers. Port harcourt ita ce birni na biyar a girma, bayan Lagos, Kano, Ibadan da Kaduna.[1][2] Bisa ga kidayar jama'a a shekarar 2006, akwai kimanin mutane 1,382,592,[3] amma an hakayo cewa akwai kimanin mutane miliyan 1,865,000 ke zaune a babban birnin. Turawan mulkin mallaka suka gina tashan jirgin ruwa a garin don daukan gawayi daga Enugu wanda ke da nisan kilomita 243 kilometres (151 mi) zuwa kasashensu na ketare, da kuma titin jirgin kasa da turawan suna gina wanda ya hade garuruwan biyu wanda ake kira da "Eastern Line".[4][5]
Kafin shekara ta 1912, wurin da ake kira Port harcourt garine na mutanen Ikwerre da Ogbulom.
Tattalin arzikin Port harcourt ya koma harkokin man fetur a yayinda aka fara fitar da mai ta jihar a shekara ta 1958. Ta hanyar gajiyar da Birnin Port harcourt ta samu daga Kamfononin man fetur na Najeriya, birnin ta samu bunkasa zuwa tsarukan gine-gine na zamani iri iri.[6]