Rabi' al-Awwal | |
---|---|
watan kalanda | |
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na | watan Hijira |
Mabiyi | Safar |
Ta biyo baya | Rabi' al-Thani |
Rabīʿ al-ʾawwal (Larabci ربيع الأوّل) shi ne wata na uku a watannin shekara na Musulunci. A cikin wannan watan Musulmai da dama kan yi bukukuwan Maulidi (bikin murnar haihuwar annabi Muhammad S.A.W). Musulmai mabiya Sunnah sun hakikance da Ranar 12 ga watan aka haifi Annabi Muhamad (s.a.w), yayinda Shi'a suka hakikance da ranar 17 ne da Asuba aka haife Shi. Annabi bai yi bikin Maulidinsa ba da kansa, sai dai ya yi nuni a Hadisi game da Musulmai su rinka azumi a ranar kowacce Litinin domin ita ce ranar da aka haifeshi. Duka dai Musulmai na girmama wannan watan.[1] {{Stub}