Arewacin Najeriya yanki ne mai cin gashin kanta a Najeriya, wacce ta sha bamban da yankin kudancin kasar, Tare da al'adunta na kanta, dangantakar ƙasashen waje da tsarin tsaro. A shekarar 1962 ta mamaye yankin Arewacin Kamaru na Burtaniya, waɗanda suka zaɓi zama a yankin ardin Arewacin Najeriya.[1]
A shekara ta 1967, An kuma raba Arewacin Nijeriya zuwa Jihar Arewa maso Gabas da Jihar Arewa maso Yamma da Jihar Kano da Jihar Kaduna da Jihar Kwara da Jihar Binuwai-Plateau, kowacce da Gwamnan ta.[2]