Adedeji Adeleke (an haife shi a ranar 6 ga watan Maris a shekarar 1956)[1][2]. Shi hamshaƙin attajiri ne a Najeriya , hamshaƙin ɗan kasuwa kuma shugaban jami'ar Adeleke.[3][4] Shi ne kuma Shugaba na Pacific Holdings Limited.[5] Shi ne mahaifin Davido, mawaƙi dan Najeriya[6][7] da Sharon Adeleke.[8] An auri Dr Vero Adeleke wanda ya rasu a ranar 6 ga Maris 2003. Ƙanin sa Ademola Adeleke shine gwamnan jihar Osun.[9]