Afirka

Afirka
General information
Gu mafi tsayi Mount Kibo (en) Fassara
Yawan fili 30,271,000 km²
Labarin ƙasa
Tsarin Daidaiton Labarin Kasa 21°05′38″N 7°11′17″E / 21.09375°N 7.1881°E / 21.09375; 7.1881
Bangare na Ostfeste (en) Fassara
Duniya
Afro-Eurasia
Afro-Asia (en) Fassara
Ƙasantuwa a yanayin ƙasa Northern hemisphere (en) Fassara
Southern Hemisphere (en) Fassara
Afirka
taswirar siyasar Afirka
yara ƴan Afrika suna murmusawa
Taswirar dake nuna yawan yarukan Afirka
sojojin Afirka dan kasar Ghana
Najeriya uwar Afirka, taswirar Nijeriya da larabci
Taswirar Afirka a shekarar 1890

Nahiyar Afirka ita ce nahiya ta biyu a fadin kasa da kuma yawan jama'a a duniya. Nahiyar da ke daya daga cikin nahiyoyi bakwai na duniya, tana da kasashe kimanin hamsin da hudu 54, kuma akwai ruwayoyi da dama da ke nuna yadda nahiyar Afirka ta samo asalin sunanta na Afirka din, to amma kuma dai ruwaya mafi inganci da kuma karbuwa a tarihi itace, wadda ke cewar, sunan Afirka ya samo asali ne daga kalmar Misirawa ta "Afru-ika" wadda ke nufin "kasar Haihuwa." Idan mutum ya kira kansa ɗan Afirka ko Ba'afirke, hakan na nuni da yadda mutum yake danganta sunansa da nahiyar Afirka a matsayin mahaifarsa. Kamar dai yadda bisa al'ada, idan mutum ya fito daga Amurka, sai a kira shi Ba'amurke, ko kuma idan daga Turai mutum ya fito sai a kira shi Bature. Haka zalika wanda ya fito daga kasashen Larabawa sai a kira shi Balarabe da dai sauransu.

African Map

Zauren taron kungiyar Tarayyar Afirka da ke birnin Addis Ababa na kasar Habasha, abun da ya kamata masu karatu su fahimta shi ne, duk da an ce sunan Afirka ya samo asali ne daga harshen mutanen Misra, to ba ana nufin harshen Larabci tsantsa ba. Domin dukkanin kasashen da ke magana da harshen Larabci kowannen su yana kuma da irin nasa karin harshen, amma tsantsar Larabci na nahawu wanda aka fi sani da 'FUSHA', Larabci ne da harshen alƙur'ani ya zo da shi.

afirka

Babu shakka haka batun yake, kuma dalilin da ya sa ma sunan Afirka din ya samu daga harshen Misiranci shi ne, kasancewar shi harshen Misirancin da dadadden harshene kuma yana da tasiri sosai akan harsuna na asali kamar su harshen Girka da na Latin, kodadai dukkaninsu ana kiran su da suna harsuna 'yan asalin indiya da Turai, wato 'Indo-European languages', a Turance kenan. Kuma ita kanta kalmar ta 'Indo' ta samu ne daga kalmar Indiya, kuma ita kalmar Indiya ta samu ne daga wajen Larabawa .lokacin da suka mamaye yankin na Indiya din. Bayan da suka gano cewa Wani mutum da ake kira Kush dan Ham, yana da 'ya'ya biyu masu suna "Hind," da "Sind." To shi Hind dan Kush sai ya kafa daula a Indiya, shi kuma 'Sind' dan Kush sai ya kafa daula a yankin Larabawa. To daga nan ne Larabawa suke kiran al'ummar Indiya da suna 'Hindu'. (Ihayatu (talk) 18:44, 31 ga watan Mayu, shekara ta 2023 (UTC)) Tarihi dai ya nunar da cewa, tasirin da harshen Misarawa yake da shi a duniyar Larabawa da ma wasu yankuna na Afirka ya samu ne sabo da yawan fina-finai da wasannin kwaikwayo da kuma wake-waken mutanen misra da suka cika yankin. Sannan kuma kamar yadda Misirawa suke kiran mutanen da suka fito daga yankin Afirka da "Afru-ika" Su kuma mutanen Latin suna kiran afirkawan ne da nasu harshen inda suke cewa da su "Africanus" Wadda ke nufin daga Afirka". To amma kuma an fara amfani da kalmar Afru-ika lokaci maitsawo kafin a fara amfani da ta Africanus. Domin kuwa tun shekaru 400 kafin haihuwar Annabi Isa Alaihis-salam, har zuwa shekaru 400 bayan komawar sa ga Allah, Rumawa sun kasance ne a arewacin Afirka. Su kuwa Girkawa sun kasance ne a Misira daga wajejen shekaru 300 kafin haihuwar Annabi Isa Alaihissalam, zuwa kimanin shekaru 200 bayan komawarsa ga Allah.


Afirka

Dodaje.pl - Ogłoszenia lokalne