Ghana ko kuma Gana ko Jamhuriyar Ghana (da Turanci: Republic of Ghana), ƙasa ce da ke a nahiyar Afirka. Ghana tana da yawan fili kimanin kilomita murabba'i 238,540. Ghana tana da yawan jama'a kimanin 27,043,093, bisa ga jimillar kidaya ta shekara ta dubu biyu da goma Sha hudu 2014. Ghana tana da iyaka da Côte d'Ivoire, Togo kuma da Burkina Faso. Babban birnin Ghana, Accra ne. Ghana ta kasance kasa mai bunkasa ta fannin ilimi da tattalin arziki a gaba daya fadin Afirka.
Nana Akufo-Addo ne Shugaban ƙasar tare da mataimakin sa Mahamudu Bawumia, daga shekara ta 2017.