Harshen Swahili | |
---|---|
Kiswahili — كِسْوَحِيلِ | |
'Yan asalin magana | 15,437,390 (2012) |
| |
Baƙaƙen boko da Swahili Ajami (en) | |
Lamban rijistar harshe | |
ISO 639-1 |
sw |
ISO 639-2 |
swa |
ISO 639-3 |
swa |
Glottolog |
swah1254 [1] |
Swahili, Anfi saninsa da Kiswahili wanda ke nufin (Harshen Mutanen Swahili), tana daga cikin Harshen Bantu kuma itace harshen farko na Mutanen Swahili. Itace harshen magana wato lingua franca a yankin African Great Lakes da wasu yankunan gabashi da kudu maso gabashin Afirka, dasuka hada da Tanzania, Kenya, Uganda, Rwanda, Burundi, Mozambique, da the Democratic Republic of the Congo (DRC).[2] harshen Comorian, da ake amfani dashi a Comoros Islands shima wani nau'in harshen Swahilin ne, dukda wasu na ganinsa a matsayin wani harshe ne daban.[3]
Ba a san ainihin adadin masu jin Swahili ba, walau na asali ne ko kuma na yare na biyu, kuma batu ne na muhawara. An gabatar da ƙididdiga daban-daban kuma sun bambanta sosai, daga miliyan 50 zuwa sama da miliyan 100. Swahili yana aiki azaman yaren ƙasa na ƙasashe huɗu: Tanzaniya, Kenya, Uganda, da JDK. Shikomor, harshen hukuma a Komoro kuma ana magana da shi a cikin Mayotte (Shimaore), yana da alaƙa da Swahili. Har ila yau Swahili ɗaya ne daga cikin harsunan aiki na Ƙungiyar Tarayyar Afirka kuma an amince da ita a matsayin harshen yare na Ƙungiyar Gabashin Afirka. Kasar Afirka Kudu ta yarda da koyar da Swahili a cikin kasar a cikin batutuwan ganin dama, za a fara a 2020.
Yawancin kalmomin Swahili ansame sune daga harshen Larabci,[4] misali Kalmar littafi a Swahili shine "kitabu", yayi daidai da Kalmar a larabci "كتاب". Dukda cewar jam'in kalmar littafi a Swahili shine "vitabu", haka daga tsarin harshen Bantu na "ki-" a matsayin Kalmar shigarwa kafi suna, wanda jam'insa shine "vi-".[5]