Muammar Mohammed Abu Minyar Gaddafi Lafazi; (/ˈmoʊəmɑːr ɡəˈdɑːfi/;. Ya rayu daga shekara ta 1942 zuwa 20 ga watan Oktoba shekara ta 2011), Muammar al-Gaddafi da larabci:
معمر محمد أبو منيار القذافي. Amfi saninsa da Konel Gaddafi ko Gaddafi, Ya kuma kasance ɗan gwagwarmayar kasar Libya ne, Ɗan siyasa, kuma mai taimakon mutanensa. Ya mulki Kasar Libiya matsayin sa na jagoran juyin mulkin da ta samar da Jamhoriyar Larabawa ta Libya wato Libyan Arab Republic da turanci, tun daga shekara ta 1969 har zuwa 1977, sannan kuma aka canja sunan jagorancinsa zuwa Shugaba Dan'uwa wato "Brotherly Leader" na babban jam'iyar talakawa, da akafi sanida Great Socialist People's Libyan Arab Jamahiriya tun daga shekara ta 1977 har zuwa shekaran 2011. Gaddafi yakasance dan rajin cigaban larabawa ne amma daga baya ana ganin ya watsar da hakan ya fara bin ra'ayin Kansa. Gaddafi ya rike mukamai da dama aciki da wajen kasarsa, daga ciki ya rike Shugaban ƙungiyar ƙasashen Afirika wato African Union (AU) daga biyu ga watan Fabrairu a shekara ta 2009 har zuwa talatin da daya ga watan Janairu.
Gaddafi yayi karatunsa a Jami'ar Kasar Libya da kuma Jami'ar Soji ta Benghazi, Gaddafi musulmi ne, mai bin ahlus-Sunnah, wato sunni Islam.