Turai | |
---|---|
General information | |
Gu mafi tsayi | Mount Elbrus (en) |
Yawan fili | 10,186,000 km² |
Suna bayan | Europa (en) |
Labarin ƙasa | |
Tsarin Daidaiton Labarin Kasa | 48°41′27″N 9°08′26″E / 48.690959°N 9.14062°E |
Bangare na |
Eurasia (en) Ostfeste (en) Duniya Afro-Eurasia |
Ƙasantuwa a yanayin ƙasa | Northern hemisphere (en) |
Turai wata nahiya ce da mafi yawanta ke Arewacin duniya da kuma kadan a yankin Gabashin duniya, wadda ke da muhimmanci a fannin tarihi, al'adu, da ci gaban kimiyya. Ta hada iyaka da Arctic Ocean daga arewa, Tekun Atalanta daga yamma, Tekun Bahar Rum daga kudu, da kuma Nahiyar Asiya daga gabas. Turai tana da fadin kasar Eurasia hade da Asiya, da kuma Afro-Eurasia tare da Asiya da kuma Afurka.[1][2] Akan bayyana rabewar Turai na Nahiyar Asiya ta kogin Tsibirin Ural, da kuma Kogin Ural, Tekun Caspian, Caucasus Mai Girma, Black Sea da kuma hanyoyin ruwa na Bosporus.
Ta shahara da kyawawan al'adu, birane masu tarihi, da kuma karfin tattalin arziki. A cikin yankin, akwai kasashe da dama masu cin gashin kansu, kowannensu na da salon mulki, harshe, da al'adun da suka bambanta.kuma suka raja a akansa