William Ruto | |||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
13 Satumba 2022 -
9 ga Afirilu, 2013 - 13 Satumba 2022 ← Kalonzo Musyoka - Rigathi Gachagua (en) →
21 ga Afirilu, 2010 - 19 Oktoba 2010
17 ga Afirilu, 2008 - 21 ga Afirilu, 2010 ← Kipruto Rono Arap Kirwa (en)
30 ga Augusta, 2002 - Disamba 2002 ← George Saitoti (en) - Moody Awori (en) →
District: Eldoret North Constituency (en) | |||||||||||||
Rayuwa | |||||||||||||
Cikakken suna | William Kipchirchir Samoei Arap Ruto | ||||||||||||
Haihuwa | Kamagut (en) , 21 Disamba 1966 (58 shekaru) | ||||||||||||
ƙasa | Kenya | ||||||||||||
Ƙabila | Kalenjin people (en) | ||||||||||||
Ƴan uwa | |||||||||||||
Abokiyar zama | Rachel Ruto (en) | ||||||||||||
Karatu | |||||||||||||
Makaranta |
Jami'ar Nairobi Kapsabet High School (en) | ||||||||||||
Harsuna |
Turanci Swahili (en) Yaren Kalenjin Kikuyu (en) | ||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||
Sana'a | ɗan siyasa da ɗan kasuwa | ||||||||||||
Imani | |||||||||||||
Jam'iyar siyasa |
United Democratic Alliance (en) United Republican Party (en) Jubilee Party of Kenya (en) Kenya African National Union (en) Orange Democratic Movement (en) |
William Kipchirchir Samoei Arap Ruto (an haife shi 21 ga watan Disamba shekarar 1966) ɗan siyasan Kenya ne wanda shine shugaban ƙasar Kenya na biyar tun ranar 13 ga watan Satumban 2022. Kafin ya zama shugaban ƙasa, ya taɓa zama mataimakin shugaban ƙasar Kenya na farko da aka zaɓa daga shekarar 2013 zuwa 2022. A baya dai ana kiran masu riƙe da muƙaman a matsayin mataimakin shugaban ƙasa kuma ba zaɓarsa akeyi ba shugaban ƙasa ne yake da haƙƙin naɗa shi. Ya taba riƙe muƙaman ministoci uku a matsayin ministan harkokin cikin gida da na noma da kuma ministan Ilimi..[1][2][3][4]
An zaɓi Ruto ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Eldoret ta Arewa daga shekarar 1997 zuwa 2007, ƙarƙashin jam'iyyar KANU da shekarar 2007 zuwa 2013 ta jam'iyyar ODM. Ya kasance Ministan Harkokin Cikin Gida a gwamnatin Daniel arap Moi daga Agusta zuwa Disamba shekarar 2002. A ƙarƙashin gwamnatin Mwai Kibaki, ya kasance Ministan Noma daga 2008 zuwa 2010 da kuma Ministan Ilimi daga Afrilu zuwa Oktoba 2010. Ruto ya tsaya takarar mataimakin shugaban ƙasa a zaɓen shekarar 2013 ƙarƙashin jam'iyyar United Republican Party, inda ya zama abokin takarar Uhuru Kenyatta daga jam'iyyar National Alliance (TNA). An sake zaɓen shi a matsayin mataimakin shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam'iyyar Jubilee a babban zaben ƙasar Kenya na 2017. Ruto ya yi nasarar tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2022, a wannan karon ƙarƙashin jam'iyyar United Democratic Alliance (UDA). A cikin tafiyar siyasar, Kenyatta ya goyi bayan abokin hamayyarsa Raila Odinga. Zaɓen dai ya fuskanci zarge-zargen tafka maguɗi a zaɓen da abokan hamayyarsa su Odinga suka yi, duk da cewa masu sa ido na ƙasa da ƙasa sun tabbatar da cewa wannan duk shaci-faɗi ne.